22 Oktoba 2020 - 12:38
​Wata Tawagar Isra’ila (HKI) Ta Isa Sudan Don Tattauna Batun Maida Hulda Da Haramtacciyar Kasar

Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa wata tawagar jami’an diblomasiyyar haramtacciyar kasar ta isa Khartum babban birnin kasar Sudan don tattauna batun maida huldar jakadanci da kasar.

ABNA24 : Wannan shirin dai yana daga cikin kokarin da Amurka take yin a tursasawa wasu kasashen Larabawa don maida hulda da HKI kafin zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a kasar ta Amurka nan da yan kwanaki masu zuwa.

Wata tashar radiyo ta HKI ta bayyana cewa tawagar ta isa Khartum a jiya Laraba, amma ba ta bayyana irin tattaunawar da suka gudana tsakanin bangarorin biyu ba.

Kafin haka dai Ministan leken asiri na haramtacciyar kasar, Eli Cohen ya bayyanawa tashar talabijin ta “Channel 13” ta kasar kan cewa nan gaba kadan kasar za ta maida hulda da kasar Sudan.

342/